Turkiya za ta kai dakarunta Afghanistan bayan janyewar Amurka - Erdogan
Shugaban Turkiya Racep Tayyip Erdogan ya ce kasar sa ce kadai za ta iya tabbatar da tsaro a Afghanistan idan Amurka ta kammala janye dakarunta daga kasar.
Wallafawa ranar:
Erdogan ya bayyana haka ne a yayin da yake shirin ganawa da shugaban Amurka Joe Biden, batun da ya ce za su tattauna akai.
Shugaban na Turkiya ya bada tabbacin cewar a shirye yake ya girke dakarunsa da bada tsaro a filin jiragen sama na Kabul babban birnin Afghanistan, inda ke zama babbar hanyar shige da ficen jami’an Diflomasiyya da ma’aikatan agaji a kasar.
Ranar Asabar kungiyar Taliban ta gargadi kasashen ketare da kada su kuskura su sake girke dakarunsu a Afghanistan bayan janyewar dakarun Amurka da na kungiyar NATO, inda kungiyar ta ce nauyin baiwa ofisoshin jakadancin kasashen ketare da filayen jiragen sama zai koma kan ‘yan kasar ta Afghanistan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu