Isa ga babban shafi
Rasha-Ukraine

Amurka ta gargadi China kan taimaka wa Rasha

Amurka ta gargadi China game da yunkurin taimaka wa Rasha a yakin da take yi da Ukraine, matukar ba haka ba kuma zata dandana kudarta.

Shugaban Amurka Joe Biden
Shugaban Amurka Joe Biden © 路透社图片
Talla

Bayanai daga Amurka na cewa ta karkashin kasa Rasha ta nemi tallafin Ukraine na karin sojoji da kayayyakin yaki, kuma China na duba yiwuwar taimaka mata, abin da a cewar Amurka zai kara tsananta yakin.

Sai dai kuma tuni ma’aikatar harkokin wajen China ta musanta zargin, inda ta ke cewa da gangan Amurka ta bullo da wannan zancen don kawai jefa ta cikin rikicin da gangan.

Wannan dai na zuwa ne bayan wata ganawa ta musamman da aka yi a tsakanin ministocin kasashen wajen Amurka da China a birnin Rome.

A yanzu haka dai bayanai na cewa za a koma ci gaba da tattaunawar zaman lafiya a tsakanin kasashen Ukraine da Rasha karo na Hudu a gobe Talata.

A cewar guda daga cikin tawagar Ukraine a tattaunawa da Rasha, Mikhailo Podolyak ta cikin wata wallafar shafin Twitter, yace yana fatan a wannan karo zaa cimma matsaya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.