Isa ga babban shafi

An gano gawarwaki kusan 300 cikin wani makeken Kabari a Ukraine

Gwamnatin Ukraine ta sanar da gano gawarwakin mutane kusan 300 da aka binne su cikin wani makaken kabari a Bucha, garin da sojojin kasar ta Ukraine suka kwace daga hannun dakarun Rasha, yayin fafatawar da bangarorin biyu suka yi a ranar Asabar.

Wani bangaren na makeken kabari dauke da gawarwakin mutane kusan 300, da sojojin Ukraine suka gano a garin Bucha.
Wani bangaren na makeken kabari dauke da gawarwakin mutane kusan 300, da sojojin Ukraine suka gano a garin Bucha. © Reuters
Talla

Magajin garin na Bucha Anatoly Fedoruk ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP ta wayar tarho cewar, gawarwakin mutane 280 aka gano binne a kabarin, yayin da kuma wasu gawarwakin ke warwatse a titunan birnin.

Tuni dai, Mataimakin ministan tsaron Ukraine Ganna Maliar ya bayyana cewa, dakarun kasar sun sake karbe ikon yankunan Kyiv baki daya bayan janyewar sojojin kasar Rasha suka mamaye yankunan tsawon makwanni.

Cikin sanarwar da ya wallafa a shafinsa ba Facebook, Mataimakin ministan tsaron na Ukraine ya lissafa, Irpin, Bucha, da Gostomel da dai daukacin yankukanan da ke kewaye da birnin Kyiv a matsayin wadanda suka samu nasarar kwacewa daga hannun dakarun Rasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.