Isa ga babban shafi
Yakin Ukraine

Rasha ta zargi Poland da yi mata makarkashiya

Rasha ta zargi Poland mai makwabtaka da Ukraine da yunkurin ta’azzara takun-sakarta da kasashen yammacin duniya bayan gwamnatin ta Poland ta kori jakadun Rasha 45 sakamakon zargin su da leken asirin kasa.

Shugaban Rasha Vladimir Putin
Shugaban Rasha Vladimir Putin Russian Presidential Press Service
Talla

Ma’aikatar Harkokin Wajen Rasha ta ce, Poland ta dauki matakin sallamar jakadun ne saboda kiyayya kuma a cewarta kungiyar tsaro ta NATO ce ta tunzura ta.

A bangare guda shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya bukaci kasashe mambobin NATO da su gaggauta gudanar da taro a birnin Brussels domin samar wa kasarsa da manyan makamai da suka hada da tankoki da jiragen yaki.

Rokon nasa na zuwa ne a yayin da aka cika wata guda cur da Rasha ta fara kaddamar da farmaki kan Ukraine.

A halin yanzu dai, kasashen na NATO na bai wa Ukraine kayayyakin tunkude hare-hare ne kawai amma ba makaman da kasar za ta iya amfani da su ba wajen mayar da martanin kan Rasha.

Wani hari na baya-bayan da Rasha ta kai a Ukraine, ya kashe fararen hula akalla shida tare da raunata fiye da dozin guda a kusa da wani gidan waya.

Ita kuwa rundunar sojin leken asiri ta Birtaniya cewa ta yi, dakarun Ukraine na samun nasarar fatattakar sojojin Rasha tare da hana su kusantar babban birnin Kyiv da suke kokarin kwacewa.

A yau Alhamis, Amurka ta sanar da lafta sabbin takunkumai kan ‘yan majalisar dokokin Rasha da wasu fitattun ‘yan siyasar kasar da kuma kamfanoni tsaro na kasar duk dai saboda wannan yakin na Ukraine

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.