Isa ga babban shafi

Za a iya shafe shakaru kafin kawo karshen yakin Ukraine - NATO

Shugaban kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg y ace yakin da ake yi a Ukraine na iya daukar shekaru da dama ba a kawo karshensa ba.

Ma'aikatan agaji yayin ceton mutanen da gini ya rushe a kansu, a birnin Borodyanka dake kusa da Kyiv babban birnin kasar Ukraine.
Ma'aikatan agaji yayin ceton mutanen da gini ya rushe a kansu, a birnin Borodyanka dake kusa da Kyiv babban birnin kasar Ukraine. AP - Efrem Lukatsky
Talla

Yayin tsokaci kan halin da ake ciki, Stoltenberg ya ce samar da makamai na zamani ga sojojin Ukraine zai taka muhimmiyar rawa wajen 'yantar da yankin Donbas na gabashin kasar daga hannun Rasha, daga hana ragowar biranen yankin shiga hannunta.

Gargadin NATOn ya zo ne a yayin da Rasha ta kara kaimi wajen kai hare-haren da zummar kwace iko da gabashin kasar ta Ukraine, ita kuwa kungiyar Tarayyar Turai ta amince da baiwa Ukraine din damar zama yar takarar shiga cikinta.

Shi ma dai, Fira Ministan Birtaniya Boris Johnson, wanda ya ziyarci Kyiv a ranar Juma'a, ya ja hankalin da cewar ga dukkanin alamu yakin na Rasha da Ukraine zai dauki tsawon lokaci, inda ya bukaci kara yawan taimakon makaman da ake baiwa kasar ta Ukraine.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.