Ukraine za ta kwato yankunanta da Rasha ta kwace - NATO
Sakataren kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg ya bayyana aniyarsa ta ganin Ukraine ta sake kwatoyankunan ta da Rasha ta mamaye ganin yadda kawayen kasar suka sha alwashin ci gaba da bata tarin taimako a wajen wani taron da Amurka ta jagoranta.
Wallafawa ranar:
Taron wanda ya samu halartar wakilan kasashe 50 da akayi a kasar Jamus, ya tattauna batutuwa da dama da suka hada da karin makamai da kayan yaki da kuma sabbin dabarun zamani da za’ayi amfani da su wajen samun nasarar yakin.
Stoltenberg ya shaidawa manema labarai cewar yanzu haka yana da yakinin cewar dakarun Ukraine na cikin yanayin da zasu iya kwato yankunan su da aka kwace.
Sakataren tsaron Amurka Lloyd Austin wanda ke jagorancin taron yace batutuwa 3 suka dauke hankalin mahalarta taron da suka hada da samar da tsaron sama a Ukraine da makamai da kuma dabarun zamani.
Sai dai kakakin Rasha Dmitry Peskov yayi watsi da taron, inda ya zargi NATO da yaudarar Ukraine.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu