Isa ga babban shafi

Amurka ta bukaci a sahale hanyar shigar Sweden cikin NATO

Amurka ta bukaci Turkiya da Hungary su gaggauta amincewa da yarjejeniyar da za ta tabbbatar da Sweden a matsayin mamba a kungiyar tsaro ta NATO, matsayar da aka shafe tsawon watanni  ba tare da an cimma mat aba, saboda rashin jituwar da ke tsakanin kasashen biyu da kasar ta Sweden. 

Shugaban kasar Amurka Joe Biden yayin wani taro a fadar White Hiouse
Shugaban kasar Amurka Joe Biden yayin wani taro a fadar White Hiouse AP - Alex Brandon
Talla

Yayin da a ranar 4 ga watan Afrilu, Finland ta samu nasarar zama memba ta 31 a NATO, Sweden na cigaba da fuskantar adawa daga Turkiya da Hungray. 

Turkiya ta da Sweden ne akan kin mika mata wasu mutane da ta zargi da hannu a yunkurin juyin mulkin aka yi wa shugaba Recep Tayyip Erdogan a shekarar 2016, wanda bai samu nasara ba, wadanda kuma shugaban je zarginsu da taimaka wa gwagwarmayar neman ‘yancin kai da Kurdawa suka shafe tsawon shekaru suna yi. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.