Isa ga babban shafi

Pentagon ta tabbatar da fitar bayanan sirrin Amurka kan yakin Ukraine

Ma’aikatar tsaron Amurka Pentagon ta tabbatar da fitar wasu bayanai da ke kunshe da tsare-tsaren kasar da kungiyar tsaro ta NATO kan dabarun taimakawa Ukraine a yakin da ta ke gwabzawa da Rasha.

Sakataren tsaron Amurka Lyord Austin.
Sakataren tsaron Amurka Lyord Austin. REUTERS - EVELYN HOCKSTEIN
Talla

Bayanan wadanda jaridun Amurka da dama ciki har da New York Times suka wallafa ranar Alhamis, na kunshe da dabarun yaki wadanda aka sabunta a watan Maris din da ya gabata kan salon da kasar ke shirin amfani da shi da taimakon NATO don tallafawa Ukraine samun nasara kan Rasha.

Pentagon ta sanar da samun rahoton fitar bayanan kuma yanzu haka ta na bincike don gano masu hannu a fitar da su, inda sakatariyar yada labaran ma’aikatar Sabrina Singh ke cewa ko shakka babu za su bankado tare da hukunta wadanda suka fitar da bayanan.

Bayanan dai sun yi yawo dandalin sada zumunta da dama musamman Twitter da Telegram wanda kunshe da alkaluman makamai manya da kanana da Amurkan ta taimakawa Ukraine dama wadanda ta ke shirin bata a nan gaba.

Haka zalika kunshin na dauke da bayanan sirri da sabbin dabarun yaki da Amurkan ke Shirin mikawa da Ukraine baya ga alkaluman yawan sojojin Ukraine da suka samu horo karkashin NATO don tunkarar yakin.

Jaridar New York Times ta ce an sabunta bayanan ne a ranar 1 ga watan Maris wanda ke dauke da alkaluman tankokin yaki 250 baya ga wasu motocin silke fiye da 350.

A cewar jaridar, cikin bayanan akwai batu kan wasu tawagar sojojin kundumbala na musamman guda 12 daga Ukraine da NATO ta basu horo na musamman.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.