Isa ga babban shafi

Zelensky ya sha alwashin kwato yankunan Ukraine 4 da Rasha ta kwace

Shugaba Volodymyr Zelensky ya sha alwashin kwato dukkanin yankunan Ukraine da Rasha ke ikirarin mayarwa karkashinta, yayinda ya bayyana cewa bazai sake tattaunawa da wani jami’in gwamnatin Moscow ba matukar Vladimir Putin na kan kujerar mulkin kasar.

Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky.
Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky. AP - Ludovic Marin
Talla

A jawabin da ya gabatar ga al’ummar kasar bayan Putin ya sanya hannu kan mayar da yankunan 4 karkashin Rasha, Zelensky ya ce zai tattauna da Rasha kan batutuwa da dama amma tare da sabon shugaba ba Putin ba.

Zelensky ya bukaci kungiyar tsaro ta NATO ta shiga rikicin gadan-gadan tare da bai wa kasar damar zama mambarta don kange ta daga makamanciyar mamayar ta Rasha.

Tuni dai shugabannin yankunan 4 da suka kunshi Lugansk da Donetsk da Kherson da kuma Zaporizhzhia suka yi mubaya'a ga shugaba Putin yayin bikin sanya hannu a dokar da ta mayar da yankunan karkashin Rasha jiya juma'a, inda aka hango yadda Putin ke musabaha da shugabannin, irin sa na farko da ya yi mu'amalar fata da fata da wasu mutane tun bayan annobar covid-19.

An dai gudanar da shagulgulan murnar dawowar yankunan 4 karkashin Rasha musamman a birnin Moscow da kuma wasu sassa da ke yankunan 4 daga bangaren masu son hadewar, kamar yadda tashoshin Rasha suka yada.

Sai dai tuni Amurka ta sanar da lafta sabbin takunkumai kan Rasha dama duk wata kasa da ta goyi bayan mamayar tata ga yankunan 4 wanda ke zuwa bayan zaben raba gardamar da al’ummomin yankin suka yi, suka kuma zabi ci gaba da zama karkashin ikon Rasha.

A cewar shugaba Joe Biden na Amurka, mamayar da Putin ya yi a Ukraine kai tsaye ya nuna irin yadda ya ke fama da kanshi yanzu haka duk kuwa da dagiyar da yake nunawa da nufin bayyanawa duniya karfinsa.

Shima sakatare Janar na kungiyar NATO Jens Stoltenberg ya yi tir da matakin na Rasha wanda ya bayyana a matsayin abin da ya sabawa doka, sai dai baiyi tsokaci game da kiran Ukraine na mayar da ita mambar kungiyar ba.

Duk da gargadin shugaba Putin na cewa zai yi amfani da karfin nukiliya wajen kare yankunan 4, amma ministan harkokin wajen Ukraine Dmytro Kuleba ya ce kasarsa za ta ci gaba da aiki tukuru wajen kare al’ummarta da ke yankunan tare da dawo da su karkashinta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.