Isa ga babban shafi

Rasha za ta kwace iko da yankunan Ukraine 4 a gobe juma'a- Kremlin

Fadar gwamnatin Rasha ta sanar da gobe juma’a a matsayin ranar da za ta kwace iko da yankunan Ukraine 4, wadanda suka kada kuri’ar raba gardamar hadewa da ita.

Shugaba Vladimir Putin na Rasha.
Shugaba Vladimir Putin na Rasha. AP - Gavriil Grigorov
Talla

Kakakin fadar ta Kremlin Dmitry Peskov ya ce yayin wani biki da zai gudana da misalin karfe 3 na ranar gobe juma’a ne shugaba Vladimir Putin ya sanya hannu kan dokar da za ta mayar da yankunan 4 karkashin ikon Moscow.

A cewar Dmitry Peskov, shugaba Putin zai gabatar da jawabi na musamman, a babban dakin taro na Georgian bayan sanya hannu akan dokar da za ta mallakawa Rasha yankunan.  

Dakarun Sojin Rasha sun mamaye yankunan Lugansk da Donetsk da Kherson da kuma Zaporizhzhia tun bayan jibgesu akan iyaka cikin watan Fabarairu.

Cikin makon nan ne, yankunan 4 suka gudanar da zaben raba gardama yayinda sakamako ya nuna cewa al’ummar yankunan sun zabi hadewa da Rasha maimakon ci gaba da zama a karkashin Ukraine.

Rahotanni sun ce yanzu haka jagororin yankunan 4 dukkaninsu sun hallara a birnin Moscow don ganawa da shugaba Vladimir Putin.

Matakin na Rasha dai na zuwa ne shekaru 8 bayan kwace iko da yankin Crimea lamarin da ya zafafa alakar kasar da takwarorinta na yammacin Turai.

Tuni dai kasashen yammacin Duniya suka gargadi Rasha kan matakin yayinda kungiyar kasashen G7 suka sha alwashin kin ayyana yankunan 4 a matsayin bangaren Rasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.