Isa ga babban shafi

EU za ta tallafa wa Tunisia da sama da Yuro biliyan daya don farfado da tattalin arzikinta

Kungiyar Tarayyar Turai za ta tallafawa Tunisia da sama da Yuro biliyan daya domin bunkasa tattalin arzikinta da kuma rage kwararar bakin haure ta tekun Meditareniya.

Shugabar hukumar tarayyar Turai Ursula von der Leyen a lokacin wata ziyarar hadin gwiwa da suka kai Tunisia da Faraministar Italiya da kuma ta Jamus.
Shugabar hukumar tarayyar Turai Ursula von der Leyen a lokacin wata ziyarar hadin gwiwa da suka kai Tunisia da Faraministar Italiya da kuma ta Jamus. AFP - -
Talla

Kasar da ke yankin arewacin Afirka, wadda ke fama da matsanancin bashi kuma take kan tattaunawa don neman wani daga asusun bada lamuni na duniya IMF, ta kasance mashiga ga bakin haure da masu neman mafaka da ke kokarin tsallakawa Turai.

Shugabar hukumar tarayyar Turai Ursula von der Leyen ce ta bayyana haka a lokacin wata ziyarar hadin gwiwa da suka kai da Faraministar Italiya da kuma  ta Jamus.

Ta ce kungiyar ta EU zata bata gudunmuwar Yuro miliyan dari 9 a cikin lokaci mai tsawo, yayinda kuma a yanzu zata bata gudunmuwar Yuro miliyan dari da 50 don inganta alakar su.

Von der Leyen ta ce bayaga inganta bangaren ciniki da zuba jarin Tunisia da kudin za su yi, hakan zai kuma taimaka wajen rufe iyakokin ta don hana masu ketawa nahiyar Turai ba bisa ka’ida ba.

Shugabar ta ce bayan kammala tattaunatar da suka yi da shugaban Tunisia Kais Saied, tana fatan bangarorin biyu za su sanya hannu a yarjejeniya gabanin babban taron kungiyar da za a gudanar a cikin wannan watan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.