Isa ga babban shafi

Tunisia ta tsamo gawarwakin 'yan cirani 36 bayan kifewar kwale-kwalensu a teku

Jami’an tsaron gabar teku a Tunisia sun sanar da tsamo gawarwakin ‘yan cirani 29 daga ruwa wadanda suka fito daga kasashen saharar Afrika, biyo bayan kifewar jiragen kwale-kwalensu 3 da ke dauke da su da nufin ratsa tekun don isa Turai.

Wasu 'yan cirani a Tunisia.
Wasu 'yan cirani a Tunisia. © AFP - Fethi Belais
Talla

Wannan dai ne shi ne ibtila’I mafi muni na baya-bayan nan da aka gani a gabar tekun na Tunisia makwanni kalilan bayan kalaman shugaba Kais Saied da ke alakanta ‘yan cirani bakar fata da suka fito daga kasashen saharar Afrika a matsayin wasu aikata manyan laifuka a kasar.

Daruruwan ‘yan cirani ke rasa rayukansu a kan hanyar ta isa Turai daga gabar tekun da ke Tunisia wadda ke matsayin hanya mafi sauki ga masu son isa turai amma kuma mai cike da hadari.

A lokuta da dama wasu akan rasa ganin ko da gawarsu bayan kifewar kwale-kwalen da ke daukarsu zuwa Turai.

Cikin wata sanarwar jami’an tsaron gabar teku a yau lahadi, ta ce ta yi nasarar ceto 11 daga cikin ‘yan ciranin wadanda ke kokarin tsallakawa Turai ba bisa ka’ida ba, bayanda jirage 3 da ke dauke da su ya kife a tsakar tekun.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.