Isa ga babban shafi

Tunisia ta karbi Yarinya 'yar shekaru 4 da ta isa Italiya ita kadai a jirgin ruwa

Jami’an tsaron gabar tekun Italiya sun mikawa Tunisia wata yarinya ‘yar shekaru 4 da ta isa tsibirin Lampedusa ita kadai daga jirgin ‘yan ciranin da ke kokarin tsallakawa Turai a watan jiya.

Tun farko mahaifin yarinyar ya rabu da ita ne a lokacin da suka kokarin hawa jirgin 'yan fasakwauri zuwa Turai.
Tun farko mahaifin yarinyar ya rabu da ita ne a lokacin da suka kokarin hawa jirgin 'yan fasakwauri zuwa Turai. REUTERS/Darrin Zammit Lupi
Talla

A jiya Alhamis ne tawagar hukumar kare hakkin kananan yara ta Tunisia ta karbi yarinyar ‘yar shekaru 4 bayan da jami’an Italiya suka yi tattaki takanas don sada yarinyar da ahalinta.

Ma’aikatar kula da harkokin Iyalai ta Tunisia cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce ta karbi yarinyar cikin koshin lafiya, bayan shafe fiye da wata guda a hannun mahukuntan Italiya, yayinda Tunis ta sanar da shirin hukunta iyayen yarinyar da suka yi sakaci da ita.

Tun farko ma’aikatar shari’ar Italiya ce ta amince da mayar da yarinyar kasar ta biyo bayan bukatar hakan daga mahukuntan Tunisia lamarin da ya kai ga zaman shari'a da ta bayar da damar mayar da yarinyar kasarta.

Rahotanni sun ce tun farko Iyalan yarinyar da suka kunshi Mahaifinta, Mahaifiyarta da kuma yayanta mai shekaru 7 sun shirya bin jirgin fasakwaurin bakin haure ta barauniyar hanya zuwa Turai, sai dai bayan isa gabar ruwa ta Sayada ne suka rabu dalilin da ya sanya mahaifin bayar da ajiyarta ga wasu bakin haure da ke wajen ba tare da sanin cewa jirgin zai tashi cikin gaggawa zuwa Lampedusa ba.

Tun a wancan lokaci ne dai jami’an tsaron Tunisia suka kame iyayen yarinyar wadanda aka tuhuma da sakacin da ya kai ga tafiya da yarinyar Turai ita kadai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.