Isa ga babban shafi

Italiya ta jaddada manufarta kan shirin tsaurara matakan karbar 'yan cirani

Ma’aikatar wajen Italy ta ce sabbin matakan da ta tsaurara kan shirin karbar bakin haure manuniya ce ga sauran takwarorinta kasashen Turai don su yi koyi da nufin magance matsalar baki daya.

Tarin bakin hauren dake dakon samun karbuwa a kasashen Turai bayan ceto su a gabar teku.
Tarin bakin hauren dake dakon samun karbuwa a kasashen Turai bayan ceto su a gabar teku. © AFP/Sameer Al-Doumy
Talla

Ministan harkokin wajen Italiyar Antonio Tajani ya ce sabbin matakan na da nufin ankarar da sauran kasashe don sanin yadda za su tunkari matsalolin na bakin haure, bayan da gwamnati Firaminista Giorgia Meloni ta ba da izini ga jiragen ruwa biyu na ceto 'yan ciranin da su isa tashar jiragen ruwa ta Sicily a karshen mako.

A tashin farko dai, gwamnatin ta Italiya ta yi umarnin sauke jirgin da ke dauke da bakin hauren da suka jikkata ne kadai gabanin amincewa da isar jiragen biyu daga bisani.

Minista Tajani ya ce kamata ya yi kasashen Norway da Jamus wadanda su ke da jiragen ceto bakin hauren su karbi sauran bakin hauren wadanda ke ci gaba da watangaririya ba tare da samun kasar da ta karbe su ba.

Tuni dai Ofishin Meloni ya fitar da wata sanarwar godiya ga Faransa wadda ta karbi bakin haure 234 bayan da suka kwashe kwanaki gabanin samun izinin sauka a tashar ruwa ta Sicily, sai dai mai magana da yawun gwamnatin Faransar Olivier Veran ya ce sam kasar ba ta amsa karbar 'yan ciranin ba domin kuwa har yanzu suna karkashin kulawar Italiya.

Italiya ta ce tana ci gaba da matsa lamba kan yarjejeniyar da aka cimma tsakanin EU da kasashen Arewacin Afirka don dakatar da bakin haure tsallakawa nahiyar Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.