Isa ga babban shafi

'Yan cirani fiye da 50 sun bace a tekun Aegean na Italiya bayan tasowa daga Turkiya

Jami’an tsaron gabar tekun Girka sun sanar da bacewar ‘yan cirani akalla 50 bayan kifewar kwale-kwalen da su ke ciki yau talata a tsakar tekun Aegean, akan hanyarsu ta shiga Italiya.

Wasu 'yan cirani da suka shiga italiya daga Turkiya.
Wasu 'yan cirani da suka shiga italiya daga Turkiya. AP - Pau de la Calle
Talla

Jami’an tsaron gabar tekun Girka sun sanar da gano kwale-kwalen a gab da tsibirin Karpathos da na Rhodes wanda ya taso daga birnin Antalya da ke kudancin Turkiya a jiya talata, gabanin igiyar ruwa ta kifar da jirgin.

Jami’an agajin da suka yi nasarar ceto ‘yan cirani 29 sun ce jirgin ya taso daga Turkiya ne dauke da mutane fiye da 80 kuma ya na kan hanyarsa ta zuwa Italiya gabanin hadarin inda zuwa yanzu ake laluben mutane fiye da 50.

Aikin ceto ‘yan ciranin da ya gudana bisa umarnin ministan harkokin ruwa Yannis Plakiotakis a cewar jami’an tsaron gabar tekun an tafi aikin kai daukin da jirage ruwa 4 sai na jami’an 2 kana jirgin saman Sojin kasar guda don laluben ‘yan ciranin.

Kakakin ma’aikatar kula da gabar teku ta Italiya Nikoa Kokalas ya ce jirgin ya kife ne sakamakon wata kakkarfar Iska da aka yi mai gudun kilomita 50 a sa’a guda wadda ta haddasa hadarin.

Mr Kokolas ya ce galibin ‘yan ciranin basa sanye da rigar kariya daga nutsewa dalili kenan da ya sanya da yawa daga cikinsu nutsewa a cikin tekun.

Ratsawa ta Turkiya zuwa Italiya na matsayin hanya mafi sauki ga ‘yan ciranin Afrika da Gabas ta tsakiya don shiga nahiyar Turai da nufin samun ingantacciyar rayuwa, wanda a kowacce rana ke haddasa asarar rayuka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.