Isa ga babban shafi
Libya-'yan cirani

Igiyar ruwa ta koro gawarwakin 'yan cirani 28 gabar teku a Libya

Rahotanni daga Libya na sanar da tsamo gawar mutane 28 da igiyar ruwa ta kado su bayan nutsewar kwale-kwalensu a kokarin bin barauniyar hanya don shiga nahiyar Turai.

Gawarwakin wasu 'yan cirani a Libya.
Gawarwakin wasu 'yan cirani a Libya. REUTERS/Hani Amara
Talla

Kungiyar agaji ta Red Crescent a Libya ta ce ta tsamo gawarwakin 28 ne a baganarori 2 mabanbanta da ke gabar ruwan Al-Alous bayan samun bayanin nutsewar kwale-kwalen ‘yan cirani, ko da ya ke ta yi nasarar ceto mutum 3 da ransu.

Majiyar da ke tababtar da labarin ta ruwaito Red Crescent na cewa bincikenta ya gano cewa an dauki kwanaki da samun nutsewar kwale-kwalen gabanin samun gawarwakin a gabar ruwan mai tazarar kilomita 90 da birnin Tripoli.

Mashigin ruwan Libya a baya-bayan nan na matsayin babbar hanyar da ‘yan cirani ke amfani da ita don tsallakawa Turai duk da yadda s uke rasa rayukansu a kowacce rana.

Wannan Ibtila’I dai na zuwa ne kwanaki kalilan bayan mutuwar ‘yan cirani 160 a dai hanyar ta Libya cikin kasa da mako guda wanda ya mayar da adadin rayukan da aka rasa cikin shekarar nan zuwa mutum dubu 1 da 500.

Hukumar kula da kaurar baki ta Majalisar Dinkin Duniya IOM wadda ke aikin kame ‘yan ciranin da ke kokarin bin hanyar mai matukar hadari don isa Turai, ta sanar da kame mutane dubu 30 a ‘yan tsakanin nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.