Isa ga babban shafi
Libya - 'Yan cirani

'Yan cirani 18 sun mutu yayin kokarin ketara teku zuwa Turai

Baki ‘yan kasashen Afirka akalla 18 da ke neman tafiyar ci rani a Turai suka mutu a gabar ruwan Libya sakamakon kifewar da kwale kwalensu yayi a kogin Mediteraniya.

Wasu bakin haure a gabar ruwan Libya
Wasu bakin haure a gabar ruwan Libya REUTERS/Ismail Zitouny
Talla

Jami’an tsaron da ke kula da gabar ruwan Zuwara mai nisan kilomita 120 daga Tripoli sun ce sun yi nasarar ceto mutane 51 da ransu.

Jami’in da ke magana da yawun jami’an ya ce bakin 18 duk ‘yan kasar Masar ne.

Tun da farko dai Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira  ta Duniya ta ba da rahoton bakin haure 16 da suka bace, ciki har da mace da yaro.

Sojojin ruwan Italiya suna ba da taimako ga bakin haure da suka bar Libya a cikin kwalekwalen da ya kife a ranar 25 ga Mayu, 2016.
Sojojin ruwan Italiya suna ba da taimako ga bakin haure da suka bar Libya a cikin kwalekwalen da ya kife a ranar 25 ga Mayu, 2016. STR / AFP

Ba a tabbatar da abin da ya haddasa nutsewar kwale -kwalen ba, amma jiragen ruwan da ke barin gabar tekun Arewacin Afirka zuwa Turai galibi na daukar fasinjoji fiye da kima, wadanda ke fara tafiya kan teku cikin dare ko da a yanayi mai tsauri don gujewa masu tsaron gabar ruwa.

Kusan bakin haure 970 ne suka mutu a kokarin shiga Turai daga Libya tun farkon shekarar nan ta 2021.

A watan da ya gabata, IOM ta ce adadin mutanen da suka mutu a kokarin ketara tekun Bahar Rum ya kusan ninki biyu a farkon rabin shekarar 2021 idan aka kwatanta da shekarar bara.

Duk da tashe tashen hankula tun bayan kifar da gwamnatin tsohon shugaban Libya marigayi Mu’ammar Ghaddafi a shekarar 2011, kasar ta zama daya daga cikin manyan cibiyoyin ficewa nahiyar Afirka zuwa Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.