Libya ta bude babbar hanyar da ta hade gabashi da yammacin kasar
Gwamnatin Libiya ta bude babbar hanyar da ta sada yankunan gabashi da kuma yammacin kasar da suka jima a rabe, sakamakon yakin basasar da ya biyo bayan kifar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Mu’ammar Gaddafi a shekarar 2011.
Wallafawa ranar:
Fira Ministan Libya Abdul Hamid Dbeibah ya jagoranci kawar da guma-guman duwatsu da kuma tarin kasar da aka yi amfani da su wajen raba yankunan na Yammaci da Gabashin Libya.
An dai shafe tsawon lokaci ana fafatawa tsakanin Sojojin Gwamnatin Libya da mayakan Janar Khalifa Haftar da ke iko da yankin gabashin kasar, kafin daga bisani a cimma yarjejeniyar sulhun da ta kai ga kafa sabuwar gwamnati a karkashin Fira Ministan Abdul Hamid.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu