Isa ga babban shafi
Libya-Faransa

Faransa ta bude Ofishin jakadancinta na Libya bayan shekaru 7

Faransa ta sake bude ofishin jakadancinta da ke birnin Tripoli na kasar Libya, bayan da aka rufe shi shekaru 7 da suka gabata saboda tashe-tashen hankulan da suka biyo bayan boren da aka yi wa gwamnatin Kanar Kaddafi.

Tsohon Ofishin jakadancin Faransa da ya gamu da farmakin 'yan tawaye a Libya.
Tsohon Ofishin jakadancin Faransa da ya gamu da farmakin 'yan tawaye a Libya. REUTERS/Ismail Zitouny
Talla

Tun cikin makon jiya ne shugaba Emmanuel Macron ya ce za a sake bude ofishin jakadancin, bayan ganawarsa da manzon gwamnatin Libya Mohamed el-Manfi.

Matakin bude Ofishin jakadancin na nuna yiwuwar tabbatuwar zaman lafiya a kasar mai fama da rikici bayan kafa gwamnatin hadin kai gabanin zaben watan Disamba.

Libya ta fada rikici ne tun bayan juyin juya halin 2011 da ya hambarar da gwamnatin kasar tare da hallaka shugaba Muammar Kaddafi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.