Isa ga babban shafi
Libya-Turai

Ministocin wajen Faransa da Jamus da Italiya na ziyara a Libya

Ministocin wajen kasashen Faransa Jamus da Italiya sun isa birnin Tripoli na Libya a kokarinsu nan una goyon baya ga sabuwar gwamnatin hadin kan kasar da ke zuwa bayan shafe shekaru ana gwabza yaki a kasar.

Firaministan Libya Abdul Hamid Dbeibah
Firaministan Libya Abdul Hamid Dbeibah Mahmud TURKIA AFP
Talla

Ziyarar wadda ke zuwa kwanaki 10 bayan kafa gwamnatin hadin kan ta Libya da za ta jagoranci kasar zuwa zaben 24 ga watan Disamba mai zuwa inda za su gana da Firaminista Abdul Hamid Dbeibah kowanne lokaci a yau Alhamis.

Ministocin 3 da suka kunshi Jean-Yves Le Drian na Faransa da Heiko Maas na Jamus da kuma Luigi Di Maio na Italiya za kuma su gana da jakadan Majalisar Dinkin Duniya na musamman a Libyan Jan Kubis gabanin jagorantar taron manema labarai na hadaka tare da takwaransu na Libyan Naila al-Mangoush.

A wata sanarwa da ministocin 3 suka fitar gabanin ganawar, Heiko Maas na Jamus ya yaba da kokarin bangarorin kasar na aminta da kafa gwamnatin hadaka, sai dai ya yi gargadin yiwuwar fuskantar tarnaki matukar ba a dabbaka wasu abubuwa da suka kamata ba.

A cewarsa bukatar samar da zaman lafiya a Libya na matsayin babban muradin kasashe da dama tsawon shekaru amma bazuwar makamai hannun daidaikun jama’a abin fargaba.

Tawagar Ministocin 3 ta ce manufar ziyarar tata bai wuce jaddada goyon baya ga sabuwar gwamnatin hadin kan ta Libya ba.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.