Isa ga babban shafi

Sojojin haya ke rike da makamai a Libya

Gwamnatin hadaka ta Kasar Libya ta bayyana cewa sojojin haya da aka gayyato daga kasashen waje dubu 20 ke rike da makamai domin taimakawa wajen kawo karshen rikice rikicen da yaki ci yaki cinyewa a Kasar ta Libya.

'yan kasar a Libya,yayin zagayowar cikon shekaru 10 da juyin -juya hali da ya kai ga kawar da Ghadafi
'yan kasar a Libya,yayin zagayowar cikon shekaru 10 da juyin -juya hali da ya kai ga kawar da Ghadafi © Aabla Jounaidi/RFI
Talla

Zagayowar mutuwar tsohon Shugaban kasar,'Yan Libya sun yi bitar cika shekaru 10 da juyin-juya-halin kasar wanda ya kai ga kawar da Muammar Ghadafi daga karagar mulki da kuma jefa kasar cikin halin tashin hankali, inda wasu daga cikinsu ke kokawa.

Rikicin da ya biyo bayan kawar da Ghadafi daga karagar mulki ya haifar da kashe dubban mutane da kuma mayar da kasar daya daga cikin mafi hadarin rayuwa sakamakon yadda 'yan bindiga suka mamaye ta.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.