Bakin haure sama 100 sun kife a gabar ruwar Libya
Fiye da 'yan cirani 100 dake cikin wani kwale-kwale ake fargaban sun mutu a gabar ruwan Libya a kokarinsu na ketarawa zuwa Turai.
Wallafawa ranar:
Kungiyoyin agaji masu zaman kansu da hukumar kula da kaura ta Majalisar Dinkin Duniya suka bayyana haka cikin wata sanarwa da suka fitar, adai-dai lokacin da masu kokarin tsallaka tekun Bahar Rum ya karu a watannin baya-bayan nan.
Kungiyoyin agaji sun zargi masu gadin gabar ruwan Libya da hukumomin Turai da gazawa wajen sauke nauyin da ke kansu na ceto rayukan bakin.
Munyi kokari amma mun nemesu mun rasa
Sai dai wani jami’in tsaron gabar ruwan Libya ya bayyannawa kamfanin dillacin labarai na Associated Press cewa sunyi kokarin neman jirgin amma suka rasa saboda karancin kayan aikinsu.
SOS Mediterranee, wata kungiyar da ke aikin ceto da jirgin Ocean Viking, ta bayyana cewa ta hango kwale-kwalen roba a yammacin Alhamis wanda ke dauke da kusan mutane 130, a Tekun na Bahar Rum da ke arewa maso gabashin Tripoli babban birnin kasar Libya .
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu