Isa ga babban shafi

Bakin haure 43 sun mutu a gabar ruwan Libya

Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa akalla bakin haure 43 daga yammacin Afrika suka gamu da ajalinsu a tekun Libya, a wani kazamin hadarin jirgin ruwa, irinsa na farko a sabuwar shekaran nan ta 2021, yayin da tace anyi nasarar ceto wasu bakin hauren 10.

An ceto wasu bakin haure a ruwar Libya
An ceto wasu bakin haure a ruwar Libya REUTERS/Antonio Parrinello
Talla

Hukumomin dake kula da ‘yan gudun hijira da sa ido kan bakin haure na majalisar dinkin duniya, sun bayyana takaicinsu dangane da mumunar lamarin da ya auku a talatan da ya gabata, kana suka ce awanni da tashin jirgin ruwan daga birnin Zawya ya kife sakamakon matsalar da injiminsa ya samu saboda rashin kyawon yanayi a teku.

Bayanan hukumomin sun kuma nuna wadanda sukayi nasarar tsira da rayukansu ‘yan asalin kasashen Najeriya, da Ghana da kuma Gambia ne, sannan tace dukkannin wadanda suka rasa rayukansu a hadarin maza ne, kuma ‘yan kasashen yammacin Afrika.

Wannan hadarin jirgin ruwa dai shine irinsa na farko da aka samu a cikin sabuwar shekaran nan ta 2021 a tekun libya, saidai ya biyo bayan hadduran da suka lakume rayukan daruruwan bakin haure dake kokarin tsallaka tekun mediterranean zuwa Turai, teku mafi hadari a duniya.

Sanarwar da wadannan hukumomin suka fitar ta kuma ce da yiwuwa adadin mamatan da aka samu a shekarar da ta gabata ya zarce yadda ake zato saboda rashin samun cikakkiyar damar sanya ido kan hanyoyin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.