Isa ga babban shafi
Turai-'yancirani

'Yan cirani 60 sun mutu a teku sakamakon tashin gobara a jirginsu

Akalla baki kusan 60 suka mutu a cikin wani jirgin ruwa sakamakon gobarar da ta tashi daga injin din jirgin a gabar ruwan Libya lokacin da yake kan hanyar zuwa Turai.

Wasu 'yan cirani a kokarin tsallakawa Turai daga Libya.
Wasu 'yan cirani a kokarin tsallakawa Turai daga Libya. REUTERS/Ismail Zitouny
Talla

Kungiyar agaji ta ‘Alarm Phone’ da ke kai dauki ga wadanda su ke fuskantar hadari a tekun Meditereniya ta ce ta yi magana da wadanda suka tsira daga hadarin inda suka shaida mata cewar wadanda suka mutu a jirgin mai dauke da mutane 100 sun zarce wadanda suka tsira.

Akalla baki sama da dubu 1 da 200 suka mutu bara akan hanyar zuwa Turai daga Afirka.

Sai dai bayanai na nuna yadda aka samu raguwar 'yan ciranin Afrika da Asiya da ke kokarin tsallakawa Turai a 2020 ko da ya ke adadin na kokarin dawowa yadda ya ke bayan matakin kasashe na sassauta dokar kulle wadda ake ganin ita ta taimaka wajen rage kwararar bakin Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.