Isa ga babban shafi
Iraqi-Poland

Iraqi ta kwaso 'yan ciraninta dubu 4 daga kan iyakar Belarus da Poland

Iraqi ta maido da ‘yan kasarta kusan dubu 4 da suka makale akan iyakokin Belarus da Poland da Lithuania da Latvia a ‘yan makwannin nan.

Galibin 'yan ciranin da suka makale a iyakar ta Poland da Belarus a kokarinsu na shiga Turai sun fito ne daga gasas ta tsakiya.
Galibin 'yan ciranin da suka makale a iyakar ta Poland da Belarus a kokarinsu na shiga Turai sun fito ne daga gasas ta tsakiya. AP - Oksana Manchuk
Talla

Tun a ranar 18 ga watan Nuwamban da ya gabata, gwamnatin Iraqi ta tashi jiragen sama guda 10 daga birnin Bagadaza zuwa Belarus domin kwaso ‘yan kasarta.

Mai Magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Iraqi, Ahmed al-Sahaf ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP cewa, jumullar ‘yan gudun hijira dubu 3 da 817 aka yi nasarar maido da su gida daga Belarus, baya ga 112 da aka kwaso daga Lithuania.

Mista Sahaf ya ce, har yanzu akwai dimibin ‘yan Iraqi da ke ci gaba da makalewa a Belarus, sannan an gaza tantance ainihin adadinsu saboda matsalar yanayin muhallinsu.

Tun  kakar da ta gabata ne, dubban ‘yan gudun hijira akasarinsu daga yankin gabas ta tsakiya musamman daga Iraqi, suka yada zango tare da kafa sansaninsu a kan iyakar Belarus da EU, yayin da suke fuskantar yanayi mai matukar wahala a fafutukarsu ta ratsawa cikin kasashen Turai.

Kasashen yammacin duniya sun zargi Belarus da kokarin bude wa ‘yan gudun hijirar kofar kwarara cikin kasashen Turai, a wani mataki na ramuwar gayya kan takunkuman da Turai ta kaka wa gwamnatin shugaba Alexander Lukashenko na Belarus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.