Isa ga babban shafi
HRW-Bakin haure

Poland da Belarus sun take hakkin dan adam kan bakin haure- HRW

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Right Watch ta ce kasashen Poland da Belarus sun karya dokoki ta hanyar azabtarwa baya ga cin mutunci dubunnan bakin hauren da ke kan iyakokinsu.

Bakin hauren da ke kokarin tsallakawa Poland daga Belarus.
Bakin hauren da ke kokarin tsallakawa Poland daga Belarus. Maxim GUCHEK BELTA/AFP
Talla

Wani rahoto da kungiyar ta fitar yau laraba ta ce gwamnatocin kasashen biyu sun tafka laifi wajen karya dokokin kare hakkin dan adam na duniya, ko da ya ke ta ce har yanzu suna da rawar takawa wajen ceto rayukan dubunnan bakin hauren da ke kan iyakar.

Rahoton Human Right Watch ya ce dole ne kasashen biyu su amince da isar da kayakin agaji ga daukacin mutanen da ke kan iyakar don gujewa ci gaba da salwantar rayuka.

Masu binciken na HRW sun ce a tattaunawarsu da mutane 19 daga cikin bakin hauren da suka fusikanci muzgunawa akan iyakar sun gano yadda jami’an tsaron kan iyakar Poland suka azbtar da mutane ta hanyar amfani da karfi wajen sake korasu Belarus.

Rahoton ya ce matakin kora bakin hauren ya sabawa dokokin bayar da mafaka na kungiyar EU.

Rahoton na HRW ya kuma roki kungiyar EU ta nuna tausayawa ga dubunnan bakin hauren da ke kan iyakar masu neman mafaka a kasashen Turai, la’akari da irin wahalhalun da s uke fuskanta wanda ke kaiwa ga rasa rayukan da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.