Isa ga babban shafi
Poland-Belarus

'Yan sandan Poland sun yi amfani da karfi kan 'yan cirani a iyakar kasar

Jami’an ‘yan sandan Poland sun yi amfani da hayaki mai sanya hawaye da kuma tankokin ruwan zafi kan dandazon ‘yan ciranin da ke kan iyaka a kokarisu na tsallakawa Turai, matakin da ya janyo cece-kuce inda Belarus ke zargin kasar da kokarin rura rikicin a bangare guda kuma Rasha ke ganin matakin ya tsabawa dokokin kare ‘yan cirani na kasa da kasa.

'Yan cirani na ci gaba da azabtuwa a kan iyakar Poland da Belarus.
'Yan cirani na ci gaba da azabtuwa a kan iyakar Poland da Belarus. AP - Oksana Manchuk
Talla

Ma’aikatar harkokin wajen Rasha ta bakin Sergei Lavrov ya caccaki matakin Poland na cin mutuncin ‘yan ciranin wanda ta ce ya sabawa dokoki kuma ba abin dauka ba ne, inda a bangare guda shugaba Alexandre Lukashenko ke cewa Poland na kokarin shafawa Belarus kashin kaji .

‘Yan ciranin wanda yawansu ya kai dubu 4 a iyakar ta Poland galibinsu daga gabas ta tsakiya, da kaso mai yawa kurdawan Iraqi, zuwa yanzu mutum 11 suka mutu akan iyakar ciki har da wata kankanuwar yarinya daga Syria.

Tuni dai kungiyar EU da Amurka suka yi barazanar sanyawa Belarus takunkumi ko da ya ke taron da suka yi a kokarin tattauna shirin sanya takunkumin ya juye na shan shayi bayan gaza daukar kwakkwaran mataki kan Alexandre Lukashenko da bangarorin ke zargi da bayar da damar kwararar ‘yan ciranin don kalubalantar EU.

Ofishin jakadancin Iraqi a Moscow ya ce sun tantance mutane 200 da Baghdad za ta jagoranci aikin kwahse su don mayar da su gida daga Belarus.

Kasashen Turai dai na zargin Belarus da hadin bakin Rasha wajen tattara ‘yan ciranin da gayya don basu damar kwarara nahiyar Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.