EU da Belarus sun tattauna rikicin bakin haure dake neman shiga Poland
Shugaban ofishin kare manufofin ketare na Kungiyar Tarayyar Turai, Josep Borrell da ministan harkokin wajen Belarus sun wata ganawa kai tsaye ta wayar tarho, game da rikicin 'yan ci-rani a karon farko, duk da cewa EU na shirin kakaba sabbin takunkumi kan fataucin bil adama.
Wallafawa ranar:
A wani sakon Twitter da Josep Borrell ya fitar ya ce dole a kawo karshen matsalolin da ake ciki a halin yanzu, yana mai cewa bai kamata a yi amfani da mutane wajen yin wata barazana ba.
Rasha
Shi ma shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi watsi da zargin da ake masa na cewa kasarsa na da hannu a rikicin, inda ya bukaci kungiyar EU da ta yi magana kai tsaye da Belarus.
Kasar Poland ta ce an tsare da dama daga cikin bakin haure da suka shiga kasar ta Belarus tare da gargadin yiwuwar wasu da dama nan gaba.
Akalla bakin 10 suka mutu
Hukumomin ba da agaji sun ce akalla bakin haure 10 ne suka mutu a kan iyakar kasar ya zuwa yanzu, kuma sun yi gargadin kalubale ga ayyukan jin kai, yayin da aka fara sassaucin tsananin sanyi.
A bangaren Belarus, hukumomi sun ce akwai bakin haure 2,000 da suka hada da mata masu juna biyu da kananan yara a sansanin mafi girma da ke kusa da kauyen Bruzgi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu