Isa ga babban shafi
Belarus - bakin haure

EU na samun ci gaba wajen tinkarar matsalar bakin haure a kan iyakar Belarus

Kungiyar Tarayyar Turai ta ce tana samun ci gaba wajen tinkarar matsalar bakin haure a kan iyakar Belarus da Poland bayan da Turkiyya ta hana 'yan wasu kasashe uku na Gabas ta Tsakiya tashi zuwa Minsk sannan Rasha ta yi watsi da barazanar Belarus na katse bututun iskar gas zuwa Turai.

Jami'an tsaron Poland kan iyakar kasar da Belarus 11/11/2021
Jami'an tsaron Poland kan iyakar kasar da Belarus 11/11/2021 via REUTERS - HANDOUT
Talla

Daruruwan bakin haure, galibi Kurdawa daga Gabas ta Tsakiya, sun makale na tsawon kwanaki a kan iyaka a cikin yanayin sanyi, inda hukumar ta lafiya ta duniya WHO ta nuna damuwa matuka game da halin da suke ciki.

Kasar Poland dai ta ki baiwa bakin damar tsallakawa, inda kasashen Yamma ke zargin shugaban Belarus Alexander Lukashenko da shigar da su cikin kasar a wani mataki dake zama tamkar martani kan takunkumi.

A mataki na farko na hana wasu bakin haure zuwa Turkiyya, Turkiyya ta ce daga yanzu ba za a bar 'yan Iraqi da Siriya da Yemen su shiga jiragen sama daga Turkiyya zuwa Belarus ba saboda "matsalolin ketarawa ba bisa ka'ida ba" zuwa cikin Tarayyar Turai.

Mataimakin shugaban hukumar Tarayyar Turai Margaritis Schinas ya shaidawa wani taron manema labarai a Lebanon cewa, "Muna ganin ci gaba ta kowane bangare."

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.