Isa ga babban shafi
Poland

Poland za ta gina katafariyar katanga don dakile kwararar bakin haure

Majalisar dokokin Poland ta amince da shirin gina katafariyar katanga a kan iyakarsu da kasar Belarus, domin dakile kwararar dubban bakin haure da ba a taba ganin irinta ba, galibinsu dake fitowa daga kasashen yankin Gabas ta Tsakiya.

Sojojin Poland yayin kafa shingen waya a kan iyakarsu da Belarus kusa da kauyen Nomiki, ranar 26 ga Agusta, 2021.
Sojojin Poland yayin kafa shingen waya a kan iyakarsu da Belarus kusa da kauyen Nomiki, ranar 26 ga Agusta, 2021. © REUTERS/Kacper Pempel
Talla

Ginin katangar zai lakume kudi kimanin Yuro miliyan 353, kuma fadin katangar zai haura kilomita 100 a kan iyakar dake gabashin kasar ta Poland.

Tun cikin watan Agustan shekarar nan ta 2021 dubban 'yan ci-rani da 'yan gudun hijira akasarinsu daga yankin Gabas ta Tsakiya da Afirka ke kokarin tsallaka kan iyakar Poland daga Belarus.

Matsalar da kungiyar EU ta zargi Belarus din da kitsawa a matsayin ramuwar gayya kan takunkuman da ta kakabawa gwamnatin shugaba Alexander Lukashenko saboda murkushe 'yan adawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.