Isa ga babban shafi
Poland

An gudanar da zanga - zangar adawa da haramcin zub da ciki a Poland

Dubban masu zanga zanga ne suka taru a birnin Warsaw da sauran sassan Poland, dare na uku a jere, jiya Juma’a, don nuna rashin amincewarsu da aiwatar da hukuncin kotu a kan haramta zubar da ciki da gwamnatin kasar mai ra’ayin mazan ke shirin yi.

Masu zanga - zangar adawa da sake fasalin tsarin mulkin Poland a Warsaw, 2018.
Masu zanga - zangar adawa da sake fasalin tsarin mulkin Poland a Warsaw, 2018. Agencja Gazeta/Slawomir Kaminski via REUTERS
Talla

Masu zanga zangar sun yi watsi da matakan kariya da hukumomin kasar suka dauka don dakile annobar coronavirus, da kuma yanayi na matsannancin sanyi da ke kasa da sifili a ma’auni Celsius, biyo bayan hukuncin kotun da ya janyo cece ku ce a ranar Laraba.

A Warsaw, masu zanga zangar sun daga tutar kasar Poland da ta kungiyar masu kare auren jinsi, da tartsatsin wuta dake alamta kungiyar mata ta Women Strike, wacce ta shirya zanga zangar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.