Isa ga babban shafi
Turai

Poland ta soke dokar zubar da ciki

Kotun fasalta kundin tsarin mulkin Poland ta haramta dokar zubar da ciki, matakin da ya gamu da suka daga ciki da wajen kasar.

mace mai dauke da juna biyu
mace mai dauke da juna biyu istock / Jovanmandic
Talla

Babbar mai shari’a kotun Julia Przylebska tace dokar da ake amfani da ita a baya ya sabbawa matakin kare rayuwar bil adama, saboda haka ta soke shi.

Wannan ya sanya Poland cikin jerin kasashen da suka haramta zubar da ciki a duniya irin su El Salvador da Congo-Brazzaville da Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo da Jamhuriyar Dominican da Masar da Gabon da Guinea Bissau da Haiti da Honduras da Laos da Madagascar da Mauritania da Nicaragua da Philippines da Senegal da kuma Suriname.

Kasashen da suka bada damar zubar da ciki lokacin uwa ke fuskantar matsala sun hada da Afghanistan da Bangladesh da Guatemala da Iraq da Cote d’Ivoire da Lebanon da Myanmar da Paraguay da Sri Lanka da Sudan da Syria da Uganda da Venezuela da Yemen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.