Isa ga babban shafi
Belarus - Diflomasiya

Lukashenko na zargin kasashen Turai da kafa sansanin ‘yan ta’adda a kasarsa

Shugaban Belarus Alexander Lukashenko ya ce hukumomin tsaron kasar sun bankado wani sansanin horas da ‘yan ta’adda na sirri a kasar, wanda bincike ya nuna cewar kasashen Jamus, Amurka, Ukraine, Poland da kuma Lithuania ke tafiyar dashi.

Shugaban kasar Belarus Alexander Lukashenko.
Shugaban kasar Belarus Alexander Lukashenko. Siarhei Leskiec AFP/Archivos
Talla

Zargin na shugaba Lukashenko na zuwa ne bayan matakin manyan kasashen kungiyar tarayyar Turai da Amurka na kakabawa Belarus takunkuman karya tattalin arziki, da zummar ladaftar da gwamnatin kasar bisa tuhumarta da amfani da karfi wajen murkushe ‘yan adawa, sai kuma karkatar da jirgin fasinjan Ryanair a cikin watan Mayu domin kama wani fitaccen mai sukar gwamnati.

Tun cikin watan Agustan shekarar bara Belarus ke fama da rikicin siyasa bayan nasarar tazarcen da shugaba Lukashenko yayi kan wa’adi na 6 a zaben da ‘yan adawa suka tsaya kai da fata kan cewar murde shi aka yi.

Alexender Lukashenko da ya share shekaru  27 yana mulkin Belarus ya sa kafar wando guda da kasashen Turai ne bayan amfani da jirgin yaki wajen tilastawa wani jirgin fasinja sauka a Minsk babban birnin kasar, inda ya kama Roman Protasevich wani fitaccen dan jarida da yayi kaurin suna wajen caccakar gwamnatinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.