Isa ga babban shafi
rASHA - POLAND

Putin ya ce Rasha ba ta da alaka da rikicin iyakar Belarus da Poland

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya musanta ikirarin cewa kasarsa na taimakawa wajen kitsa rikicin da ya haifar da daruruwan bakin haure daga Gabas ta Tsakiya a kan iyakar Belarus da Poland.

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin yayin taron APEC da ya halarta ta fasahar bidiyo 2/11/21.
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin yayin taron APEC da ya halarta ta fasahar bidiyo 2/11/21. Mikhail Metzel Pool/AFP
Talla

Da yake dora alhakin rikicin yankin gabas ta tsakiya kan manufofin kasashen yammaci, Putin ya mayar da martani ga ikirarin da Poland da sauran su ke yi na cewa Rasha na aiki tare da Belarus don matsa lamba kan iyakar Tarayyar Turai.

"Ina son kowa ya sani, babu ruwan mu da wannan matsala," kamar yadda ya shaida wa gidan talabijin na kasar.

Putin ya ce akwai bukatar shugabannin kasashen Turai su tattauna da shugaban kasar Belarus Alexander Lukashenko domin warware rikicin kuma "yana mai yakinin cewa " shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a shirye take ta yi hakan.

Bakin hauren wadanda akasari Kurdawa, sun makale ne na tsawon kwanaki a kan iyakar kasar cikin yanayi na sanyi da ke neman zama kankara , inda suka kafa tanti tare da kona itace domin samun dumi.

Belarus ta ce akwai kimanin mutane 2,000 a sansanin da suka hada da mata masu juna biyu da kananan yara, yayin da Poland ta ce akwai bakin haure tsakanin 3,000 zuwa 4,000 a kan iyakar, inda wasu ke zuwa kusan   kowace rana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.