Poland ta zargi Belarus da sauya dabaru kan matsalar bakin haure
Kasar Poland ta ce Belarus ta sauya dabarunta a rikicin kan iyaka inda a yanzu take tura ‘tsirurun 'yan ci-rani zuwa wurare da yawa a kan iyakar gabashin Tarayyar Turai.
Wallafawa ranar:
Ko da yake akwai alamun samun saukin rikicin, Ministan Tsaron kasar Mariusz Blaszczak ya ce yana sa ran za a dade ana fama da rikicin kan iyakar.
Jami'an tsaron kan iyakan Poland sun sanar da cewa wani sabon yunkurin tsallaka kan iyakar ya hada gungun 'yan ci-rani da dama, dake diban tsariro zuwa mashigi daban-daban ko da yake akwai mai kunshe da taron mutane 200 da ke jifa da duwatsu da kuma amfani da hayaki mai sa hawaye.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu