Isa ga babban shafi
Poland-bakin-haure

Poland ta yi gargadin cewa za a dade ana rikicin baki-haure

Kasar Poland ta yi gargadin cewa rikicin bakin haure da ya taso ka iya kwashe shekaru ana fama da shi, batun da ke zuwa kwana guda bayan da jami’an tsaron kasar suka harba hayaki mai sa hawaye kan dandanzon bakin haure dake kan iyakar kasar da Belarus.

Bakin-haure da suka taru a kan iyakar Poland da Belarus.
Bakin-haure da suka taru a kan iyakar Poland da Belarus. Oksana MANCHUK BELTA/AFP
Talla

Ministan tsaron Poland Mariusz Blaszack ya ce abin ya tsananta cikin dare, yayin da bakin hauren suka yi yunkurin fin karfin jami’an tsaro wajen shiga kasar da karfin tuwo.

Wannan ce ta sanya Poland din ta yi gargadin cewa lamarin ka iya kwashe tsawon watanni ko ma shekaru ana fama da shi, matukar ba’a yi hattara ta hanyar hadin kai tsakanin kasashen turai don tunkarar matsalar ba.

A cewar sa barazanar shiga kasar da karfin tuwo da bakin hauren suka nuna shine ya tilasta wa jami’an tsaron jefa musu hayaki mai sa hawaye, da kuma watsa musu ruwan zafi.

Tun a makon da ya gabata ne dai dubban bakin haure, mafi yawan su daga gabas ta tsakiya suka yi cincirindo a kan iyakar Belarus da Poland din, abin da ake ganin da shugaban kasar Belarus Alexandra Lukashenko ne ya sako su da gan-gan.

Zargin da tuni Alexandra Lukashenko da takwaransa na Rasha Vladmir Putin suka musanta, tare da caccakar tarayyar Turai da rura wutar rikicin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.