Isa ga babban shafi
EU-Belarus

EU na shirin ladabtar da Belarus saboda bakin-haure

Kungiyar Tarayyar Turai ta jadadda kudurinta na sanya wa kasar Belarus karkashin jagorancin shugaba Alexandra Lukashenko takunkumi, sakamakon zargin sa da jibge bakin-haure kan iyakar kasar da Poland da nufin angiza su shiga Turai.

Shugaban Belarus Alexander Lukashenko
Shugaban Belarus Alexander Lukashenko Maxim GUCHEK BELTA/AFP
Talla

A cewar Tarayyar Turai ratsawa zuwa wata kasa ba bisa ka’ida ba babban kuskure ne kuma laifi ne gagarumi, a don haka ba za su zuba idanu Lukashenko ya jefa yankin cikin tashin hankali kawai saboda biyan wata bukata tasa ba.

Idan dai za a iya tunawa tun a makon jiya ne aka fara tada jijiyoyin wuya a tsakanin tTrayyar Turai da Lukashenko, bayan zargin sa da take-taken haddasa rikici a Turai da gan-gan ta hanyar sakin bakin haure daga kasarsa.

Sai dai a wata tattaunawa da Ministocin Kasashen Kungiyar Tarayyar Turai suka yi, sun amince cewa za su fadada takunkumin da suke shirin sanya wa Belarus har zuwa kan wasu manyan kamfanoni da  kasashen da ke  goya wa Belarus baya cikinsu kuwa har da dai-dai kun mutane.

To amma dai har aka kai ga karshen taron ba a  cimma matsaya kan irin takunkumin da za a kakaba wa Belarus din ba, sannan kuma ba a bayyana karin mutanen da za a hada su cikin sanya takunkumin ba, wanda ake ganin zai shafi manyan jakadun kasar 30 da suke aiki a kasashen Tarayyar Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.