Isa ga babban shafi
Poland-Belarus

Poland ta ki zama da Belarus kan matsalar kwararar baki

Firaministan Poland Mateusz Morawiecki ya nuna adawarsa da shiga tattaunawa kai-tsaye da shugaban Belarus Alexander Lukashenko don kawo karshen rikicin ‘yan ci-rani tsakanin Belarus da kuma kasashen Turai.

Wasu daga cikin bakin haure masu neman fantsama cikin Turai
Wasu daga cikin bakin haure masu neman fantsama cikin Turai © Maxim Guchek/BelTA/Handout via REUTERS
Talla

A cewar Firaminista Morawiecki, matukar kasashen Turai suka amince da shiga tattaunawa da Lukashenko, hakan na nufin cewa sun amince da zaben da aka yi masa a matsayin halastaccen shugaban kasar Belarus.

Gargadin na Firaministan Poland na zuwa ne sa’o’i kadan bayan da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta tattauna ta wayar tarho da shugaba Lukashenko, karon farko da shugaban wata kasa ta yammacin duniya tun bayan zanga-zangar da ta biyo bayan zaben da aka yi masa.

Har ila yau Merkel ta yi irin wannan zantawa da shugaba Vladimir Putin na Rasha dangane da matsalar ‘yan ci-rani a kan iyakar Belarus da Poland.

Yanzu haka mahukuntan kasar ta Poland sun ce, akwai daruruwan ‘yan ci-rani da suka yi nasarar tsallaka iyakar kasar ta Poland, yayin da mahukuntan kasar ke cewa sun cafke sama da 100.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.