Isa ga babban shafi

'Yan sanda a Tunisia sun tarwatsa masu zanga-zanga kan bacewar 'yan cirani

‘Yan Sanda a Tunisia sun yi amfani da hayaki mai sanya hawaye wajen tarwatsa dandazon masu zanga-zangar da ke kokarin kaiwa tsibirin Djerba da ake gudanar da taron kasashe 18 renon Faransa, don nuna bacin ransu da bacewar ‘yan ciranin kasar cikin watan Satumba.

Masu zanga-zanga a Tunisia.
Masu zanga-zanga a Tunisia. REUTERS - ZOUBEIR SOUISSI
Talla

Dandazon masu zanga-zangar sun rika daga allunan da ke dauke da rubutun kalubalntar yadda rayukan tarin bakin haure ke salwanta a teku ba tare da mahukunta sun dauki matakan da suka dace ba.

Zanga-zangar na fatan samar da mafita ga tarin ‘yan ciranin kasar da ke ratsa teku zuwa Turai a kowacce rana inda da dama daga cikinsu ke rasa rayukansu a kan hanya.

Tsakanin ranakun 20 zuwa 21 ga watan Satumban da ya gabata ne matasa ‘yanciranin Tunisia 18 daga gabar ruwan kudu maso gabashin Zarzis suka hau wani jirgin ruwa tare da ratsa teku a kokarinsu na kaiwa gabar Italiya don shiga Turai amma har zuwa yanzu gawarwakin mutum 8 kadai aka iya ganowa.

Iyalai da ‘yan uwan ‘yan ciranin na ci gaba da matsa kaimi ga gwamnatin kasar don ganin ta tura tawagar masu bincike ta musamman da nufin lalubo gawarwakin sauran mutum 10 da ke cikin jirgin.

Masu zanga-zangar da goyon bayan Masuntan gabar ruwan ta garin Zarzis sun sha alwashin hana hada-hada a ilahirin yankin har sai an dauki matakin aikewa da tawagar bincike don gano gawarwakin sauran ‘yan ciranin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.