Isa ga babban shafi

Ana zaben raba gardama a Tunisia

A wannan Litinin al'ummar Tunisia ke kada kuri'a kan sabon kundin tsarin mulkin da shugaba Kais Saied ya gabatar, wanda aka zarge shi da bai wa ofishinsa iko fiye da kima tare da yin barazanar kafa tsarin mulkin-kama karya a kasar.

Shugaban Tunisia Kais Saied na kada tasa kuri'ar.
Shugaban Tunisia Kais Saied na kada tasa kuri'ar. AP - Slim Abid
Talla

Kuri'ar raba gardamar na zuwa ne shekara guda bayan da Saied ya kori majalisar zartarwarsa da kuma dakatar da majalisar dokokin kasar, lamarin da 'yan adawa ke kallo a matsayin juyin mulki.

Kodayake da dama daga ‘yan kasar na maraba da yunkurin nasa duk kuwa da tabarbarewar tattalin arziki da rudanin siyasa da kuma tsarin da suke ganin bai kawo wani ci gaba a rayuwarsu ba cikin shekarun da suka gabata, tun bayan hambarar da mulkin kama-karya na Zine El Abidine Ben Ali a shekara ta 2011.

Akwai tsiraru da ke da shakkun kada kuri'a a zaben, to amma fitowar jama'a za ta auna irin farin jinin Saied bayan shekara guda da ya yi yana kara tsaurara tsarin mulki shi kadai wanda ba a ga wani ci gaba ba wajen tinkarar matsalolin tattalin arzikin kasar da ke arewacin Afirka.

Da yake ganawa da manema labarai a safiyar Litinin din nan, Saied ya shaida musu cewa kasar na gudanar da muhimmin zabe da ke cike da tarihi na bada ‘yanci.

Kimanin mutane miliyan 9 da dubu dari 3 ne daga cikin ‘yan kasar miliyan 12 suka cancanci kada kuri'a.

Sabon kundin tsarin mulkin zai bai wa shugaban kasar damar kasancewa a matsayin kwamandan rundunar soji, haka nan zai ba shi damar nada gwamnati ba tare da amincewar majalisar dokoki ba, sannan kuma zai ba shi kariya daga duk wata barazanar tsigewa daga matsayinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.