Isa ga babban shafi

Zanga-zangar adawa da manufofin Shugaba Kais Sa'id na Tunisia

Dubban yan kasar Tunisiya ne suka gudanar da zanga-zanga a birnin Tunis a jiya asabar don yin tir da manufofin shugaba Kais Sa'id, wanda suke zargin shi ne ke da alhakin tabarbarewar tattalin arzikin kasar, wanda ke fuskantar matsalar karancin kayan masarufi da hauhawar farashin kayayyaki.

Wasu daga cikin masu zanga-zanga  da yan Sanda a Tunisia
Wasu daga cikin masu zanga-zanga da yan Sanda a Tunisia REUTERS - ZOUBEIR SOUISSI
Talla

A karkashin jagorancin jam'iyyar National Salvation Front, gamayyar jam'iyyun adawa masu zanga-zangar sun tsallaka manyan titunan babban birnin Tunisiya, suna kira da shugaban ya yi murabus.

Wannan zanga-zangar tana nuna fushin halin da ake ciki a Tunisiya karkashin Kais Saied da kuma kira da  ya yi murabus, kamar yada tsohon Fira Minista Ali Laaraydh, mataimakin shugaban Ennahdha, ya shaida wa manema labarai.

A dai-dai lokacin da jama’a ke gudanar da wannan zanga-zanga ,asusun ba da lamuni na duniya IMF ya cimma yarjejeniya da gwamnatin kasar ta Tunisia wadda za ta bada damar biyan dala biliyan 1.9 yayin da Tunisia ke fama da matsananciyar matsalar tattalin arziki.

An dai amince da wannan ka'ida ne tsakanin ayyukan fasaha na asusun ba da lamuni na duniya IMF da hukumomin Tunisia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.