Isa ga babban shafi

Yan adawa a Tunisia sun kalubalanci matakin shugaba Saied

Yan Sanda a birnin Tunis na kasar Tunisia sun tarwatsa masu bore dake adawa da matakin Shugaban kasar na shirya zaben jin ra’ayin mutan kasar a watan Yulin wannan shekara.

Yan Sanda na tarwatsa masu zanga-zanga a Tunisia
Yan Sanda na tarwatsa masu zanga-zanga a Tunisia AFP - FETHI BELAID
Talla

Yan Sanda sun hana masu zanga-zanga karasawa harabar ofishin babban hukumar  zabe mai zaman kanta  dake birnin na Tunis.

Ranar 22 ga watan Afrilu ne Shugaban kasar ya nada wasu daga cikin wakilan hukumar shirya zaben kasar,matakin da yan adawa suka kalubalance shi,ya rusa majalisa tare da sallamar alkalan kotun dama kaucewa biya musu bukatun su ,al'amarin da yan adawa ke kalo a matsayin wanda ya sabawa kudin tsarin mulkin wannan kasa ta Tunisia.

Hukumar zabe da Shugaban kasar ya nada Shugaban ta,matakin da yan adawa ke ci gaba da yi tir da Allah wadai.

Wasu daga cikin masu zanga-zangar na dauke da aluna da ake iya karanta cewa hukumar Shugaban kasa da ta yi dai-dai da hukumar shirya magudi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.