Isa ga babban shafi
Tunisia

'Yan adawa sun yi wa shugaban Tunisia Ca

‘Yan adawa a Tunisia sun yi Allah wadai da matakin da shugaban kasar Kais Saied ya dauka na tsawaita haramcin da ya yi wa Majalisar Dokoki, wanda suke dangatawa da yi wa dimokiradiya targade.

Shugaban Tunisia Kais Saied
Shugaban Tunisia Kais Saied FETHI BELAID AFP
Talla

Shugaba Saied ya bayyana aniyarsa ta ci gaba da aiwatar da sauye-sauye a tsarin siyasar kasar, bayan kawar da Majalisar Ministoci da kuma dakatar da majalisa tare da bai wa kansa karfin fada aji da kuma mulki ba tare da wadannan bangarori ba.

Shugaban ya kuma bayyana shawarar da yake yi na kawar da kundin tsarin mulkin kasar, yayin da yake cewa majalisar za ta ci gaba da zama a rufe har zuwa ranar 17 ga watan Disambar badi da za a gudanar da sabon zabe.

Yayin da wasu ‘yan kasar da suka gaji da yadda ‘yan siyasa ke jagorancin kasar da kuma yadda cin hanci ya dabaibaye su, ke bayyana farin cikinsu da matakan da shugaban ke dauka, wasu na adawa da shirin, abin da ya haifar da zanga-zanga a ciki da wajen kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.