Isa ga babban shafi
Tunisia-Zanga-zanga

An gudanar da zanga-zanga a Tunisia bayan shugaba ya kara wa kansa karfi

Dubban al’ummar Tunisia sun gudanar da zanga-zangar adawa da matakin shugaba Kais Saied bayan matakinsa na baya-bayan da ke sake kara wa kansa karfin iko fiye da sashen shari’a lamarin da bangaren adawa ke kallo a matsayin kama karya.

Masu zanga zanga a birnin Tunis na Tunisia.
Masu zanga zanga a birnin Tunis na Tunisia. AP - Hassene Dridi
Talla

Karkashin wani kudirin doka da Kais Saied ya sanar ba tare da sahalewar Majalisa ba, shugaban ya rushe hukumar kula da al’amuran shari’a na kasar wanda ya bashi karfin iko iya hana nadin alkalai tare kuma da haramta musu shiga yajin aiki.

Sa’o’i bayan sanar da wannan mataki a jiya lahadi, al’ummar Tunisia fiye da dubu 2 sun yi dandazo a tsakar birnin Tunis galibinsu riko da tutar kasar tare da rera wakokin kalubalantar abin da suka kira kama karyar shugaban.

Masu zanga zangar na Tunisia sun rabu gida biyu ta yadda wasu ke tambaya cikin wake wasu kuma na amsawa suma dai a cikin waken.

Rukunin farko na masu zanga-zangar cikin sigar tambaya na rera wakar cewa al’ummar Tunisia me kuke sai rukuni na biyu ya amsa da cewa kawo karshen kama karyar gwamnati, kwatankwacin juyin juya halin gwamnatin Zine El Abidine Ben Ali shekaru 10 da suka gabata, matakin da ke nuna cewa suna bukatar faduwar gwamnatin.

Wani rukuni daban na masu zanga-zangar na rera waken bukatar ceto demokradiyyar kasar.

Matakin na Kais Saeid na zuwa ne mako guda bayan shugaban na Tunisia ya sha alwashin rushe babbar majalisar shari’ar kasar wadda ya zarga da assasa zanga-zanga a kasar. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.