Isa ga babban shafi
Tunisia

An gudanar da zanga-zangar adawa da juyin mulki a Tunisia

Dubban 'yan Tunisia ne suka taru a kusa da majalisar dokokin kasar a yau Lahadi domin nuna adawa da kwace ikon mulkin shugaban kasa da suka kira juyin mulki.

Wasu masu zanga-zangar adawa da gwamnatin Tunisia.
Wasu masu zanga-zangar adawa da gwamnatin Tunisia. FETHI BELAID AFP
Talla

Wannan dai shi ne gangami na baya-bayan nan da ke adawa da matakin da shugaba Kais Saied ya dauka a ranar 25 ga watan Yuli na korar gwamnati, dakatar da majalisar dokoki da kuma kwace madafun iko, saboda wata babbar barazana ga kasar da aka fara boren kasashen Larabawa na nuna adawa da mulkin kama karya a shekara ta 2011.

Masu zanga-zangar sama da 3,000 ne suka taru, suna ta kururuwar cewa su na son a kawo karshen juyin mulkin da kuma aikin shugaba Kais da ke kokarin haifar da yakin basasa, tare da bayyana shugaban kasar a matsayin "wakilin mulkin mallaka.

Kamfanin dillancin labarai na Faransa, ya ruwaito cewa wasu daga cikin fusatattun masu zanga-zangar na dauke da alluna da ke nuna adawa da yiwa kafafen yada labarai barazana da kuma neman Hukumar shari'a mai zaman kanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.