Isa ga babban shafi
Tunisia

Shugaban Tunisia ya kafa sabuwar majalisar ministoci

Shugaban Tunisia Kais Saied ya nada sabuwar Majalisar Ministocin kasar bayan kusan watanni uku da ya karbe iko na gudanar da kusan dukkan harkokin mulkin kasar.

Shugaba Kais Saied a yayin gabatar da jawabinsa ta kafar talabijin
Shugaba Kais Saied a yayin gabatar da jawabinsa ta kafar talabijin - AFP
Talla

A jawabin shugaban wanda aka yada kai tsaye ta tashar rediyo da talabijin na kasar, Shugaba Saied ya rantsar da Uwargida Najla Bouden , mace ta farko  a kasar a matsayin Firaminista.

A jawabinta na farko ta sanar cewa, batun yakar cin hanci da rashawa zai kasance a kan gaba da za su bada fifiko akai.

Bouden ta kuma lashi takobin inganta rayuwar al’umar Tunisia, da maido da daraja da mutuncin gwamnatin kasar.

A ranar 25 ga watan 7 ne dai, shugaban kasar ya kori tsohon Firaminista sannan kuma ya rusa Majalisar Dokokin kasar, a wani babban garambawul da ya yi, inda ya kwace dukkan karfin gwamnatin a hannunsa shi kadai.

Sau da yawa, ya kan soki kundin tsarin mulkin kasar wanda ake amfani da shi tun shekara ta 2014, wanda ya yamutsa tsarin mulkin demokuradiya na shugaba mai cikakken iko da kuma tsarin Firaminista.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.