Isa ga babban shafi
Tunisia

'Yan Tunisia sun sake yin zanga-zanga kan dakatar da majalisar dokoki

Daruruwan masu zanga -zanga sun yi gangami a babban birnin Tunisia don nuna adawa da matakin Shugaba Kais Saied na mamaye ikon gwamnatin kasar baki daya.

Masu zanga-zanga a Tunis babban birnin kasar Tunisia.
Masu zanga-zanga a Tunis babban birnin kasar Tunisia. AP - Hassene Dridi
Talla

Masu zanga-zangar da a ranar lahadi suka yi dandazo a tsakiyar birnin Tunis, sun yi tattakin ne cikin tsauraran matakan tsaro, domin dakile barazanar barkewar kazamin bore.

Zanga -zangar dai ita ce ta biyu tun lokacin da shugaba Saied ya kori ya dakatar da majalisar dokokin kasar a ranar 25 ga Yuli, kafin daga bisani ya kori Firaministan sa kana kuma ya nada kansa a matsayin mai gabatar da kara.

Kimanin kungiyoyin kare hakkin dan adam na kasa da kasa da na Tunisia 20 ne suka yi tir da matakin na shugaba Kais Saed.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.