Isa ga babban shafi
Tunisia

'Yan Tunisia sun yi zanga-zanga kan dakatar da majalisar dokoki

Daruruwan masu zanga -zanga sun yi tattaki a birnin Tunis yau Asabar don neman janye dakatarwar da shugaban Tunusia Kais sa’id ya yiwa majalisar dokoki kasar a watan Yuli.

Daruruwan masu zanga -zangar adawa da dakatar da majalisar dokokin Tunisia da shugaba Kais Saed yayi, a akan titin Bourguiba da ke birnin Tunis. 18 ga Satumba, 2021.
Daruruwan masu zanga -zangar adawa da dakatar da majalisar dokokin Tunisia da shugaba Kais Saed yayi, a akan titin Bourguiba da ke birnin Tunis. 18 ga Satumba, 2021. AFP - FETHI BELAID
Talla

Kamfanin Dillancin Labarai na AFp ya ruwaito cewa zanga zangar ta gudana ne cikin tsauraran matakan tsaro.

Galibin masu zanga-zangar dai magoya bayan jam'iyyar adawa ta Ennahdha ce, mai rinjaye mafi girma a majalisar dokokin Tunusia kafin dakatar da ita da shugaba sa’id yayi.

A ranar 25 ga watan Yuli shugaba Kais Sa’ed ya dakatar da majalisar dokokin Tunisia ta re da cirewa ‘yan majalisar rigar kariya, sannan kuma ya mai da kansa shugaban masu gabatar da kara, bayan da ya zargi jagororin kasar da dama da zama miyagu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.