Isa ga babban shafi
Tunisia

Masu fafutuka na fargabar halin da yancin dan adam zai shiga a Tunisia

Masu fafutuka sun ce akwai fargaba a game da batun yanci a Tunisia, a yayin da shugaba Kais Saied ke ci gaba da kama wadanda ake gani abokan hamayya ne, bayan da ya kori gwamnatin kasar tare da dakatar da majalisar dokoki.

Kaïs Saïed, shugaban Tunisia.
Kaïs Saïed, shugaban Tunisia. AFP - KARIM JAAFAR
Talla

Har  yanzu shugaba Saeid  bai kai ga bayyana shirinsa a kan matakin korar gwamnatin kasar da ya dauka ba, duk da bukatar hakan da jam’iyyun siyasa suka yi ta mikawa.

‘Yan siyasa da dama da ma ‘yan kasuwa, har ma da alkalai da ‘yan majalisar dokokin da suka rasa kariyar da kundin tsarin mulki ya ba su bayan da Shugaba Saeid ya dakatar da su, sun ce an haramta musu ficewa daga kasar, yayin da aka wa wasu daga cikin su daurin talala, lamarin da ya janyo caccaka daga masu fafutuka.

Matakin mai ban mamaki da Saied ya dauka ya haifar da rashin tabbas a Tunisia, makyankyasar juyin juye hali ta kasashen Larabawa da  ya kunno kai shekaru 10 da suka wuce, lamarin da ya assasa tada kayar baya daga masu rajin kare dimokaradiyya a yankin da ya kai ga sauke shugabanni da suka yi mulki da takalmin karfe.

Tunisia, wadda ake jinjina wa a sakamakon nasarar da ta samu wajen tafiyar da mulkin dimokaradiya a gabas ta Tsakiya da ma Arewacin Afrika ta stinci kanta a cikin dabaibayi na rikicin siyasa da matsin tattalin arziki, da kuma annobar Covid -19.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.