Isa ga babban shafi
Tunisia

Tarzomar siyasa ta barke a Tunisia

Tarzoma ta barke a harabar Majalisar Dokokin Tunisia da sojoji suka mamaye, kwana guda bayan da shugaban kasar Kais Saied ya sauke Firaminista, ya kuma dakatar da majalisar, lamarin da ya jefa jaririyar dimokaradiyyar kasar cikin rikicin tsarin mulki.

Masu tayar da kayar baya a harabar Majalisar Dokokin Tunisia
Masu tayar da kayar baya a harabar Majalisar Dokokin Tunisia AP - Hassene Dridi
Talla

Saied ya sauke Firaminista Hichem Mechichi daga mukaminsa, ya kuma yi umurnin a rufe majalisar dokokin kasar na tsawon kwanaki 30, matakin da jam’iyya mafi girma a kasar ta Ennahdha ta bayyana a matsayin juyin mulki.

Da safiyar Litinin din nan sojoji suka dakile hanyoyin shiga majalisar a birnin Tunis, yayin da a wajen majalisar, magoya bayan shugaban kasar suka yi ta jifa da duwatsu da munanan kalamai kan jami’an jam’iyyar Ennahdha da ke zaman dirshen a wajen majalisar kan matakin dakatar da ita da shuguaban kasar ya yi.

Wannan matakin na shugaba Saied, shekaru 10 bayan juyin-juya halin Tunisia da aka wa lakabi da Arab Spring na zuwa ne duk da cewa kundin tsarin mulkin kasar ya fifita Firaminista a kan shugaban kasa, ta wajen takaita ikon shugaban ga batutuwan da suka shafi tsaro da diflomasiyya.

Wannan rikicin ya biyo bayan gutsiri-tsoma ne da aka dade ana yi tsakanin shugaban kasar da Fiiraminista da kuma shugaban jam’iyyar Ennahdha Rached Ghannouchi, lamarin da ya gurgunta matakan kariya daga annobar Korona, a yayin da take ta’azzara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.